MALAMAN TSUBBU DA BOKAYE SU SUKE INGIZA MASU YIN FYADE
Alhamdulillahi Rabbil Aalameen
Dukkan yabo da Godiya sun tabbata ga Allah Ubangiji Mara farko Mara karshe Wanda tsawon zamani baya riskar shi, tsira da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad saw da iyalan gidansa da Sahabbansa da Sauran masu koyi dasu bi da bi har zuwa ranar Al-qiyama Allah kasa muna Cikin su.
Assalamu Alaikum Warahmatullah, bayan Haka Ina Mai alhini game da abubuwan da muka tsinci kanmu a ciki na damuwa musamman akan yadda Bokaye da Malaman Tsubbu suke kokarin rushe Al'umma ta hanya kawar dasu akan karantarwa musulunci na tsarin gidan iyali da Kuma tsare mutunci da martabar Mata ta Hanyar Basu cikakken yanci a islam ba kamar yadda yan Gwagwarmayar nemowa Mata yanci ke ikirari ba ta hanya fito da matan kan titi da nuna musu cewa su kyamaci aure ba, ko Kuma duk Abunda Namiji zai iya mace ma zata iya can a bakin su.
Islam ya tsara Mana Babu wata hanya da Mutum zai bi ya sadu da mace sai ta Hanyar aure bisa ka,idojin musulunci da karantarwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (saw) Kuma Dole aure ba zai yiwu ba sai yadda karantarwar musulunci ya tanadar, ba kamar yadda yahudawa ke Fadi ba cewar idan mace ta Kai Shekaru 18 tana da yanci kwanciya da Namijin data ga dama bisa yadda da amincewarta ba tareda aure ba, a wajen su wannan ba laifi bane Amma a musulunci addinin Gaskiya wannan laifi ne babba Wanda Allah ya haramta kusantarsa balle Kuma aikatawa.
Lokacin ya tsawaita zarmewa da son Duniya Wanda Shedan ya kawatawa mutane Yan Duniya Wanda suka manta da Allah da kuma ranar Qiyama Bokaye da Malaman Tsubbu sun halakar dasu ta Hanyar mayar dasu tamkar dabbobi ace Wai Mutum magidanci ko matashi Mai ganiyar karfi ya zauna ya kashe Zuciyarsa yaqi neman Sana,ar da zai Kare mutuncinsa Dana iyalinsa ga magidanci, matashi Kuma ya nema kudin halal Dan ganin cewa ya mallaki Matar aure ta Hanyar halal.
Bokaye da Malaman Tsubbu sun nuna musu cewar bin kananan yara ana yi musu fyde wata hanya ce ta samun dukiya ba tareda Shan wahala ba shi yasa a Yan kwanakin Nan ake ta samun yawaitar yiwa kananan yara fyde ko Kuma kaga Mahaifi ya yiwa yarsa karama fyde ko Kuma yayi Zina da yarsa ta cikinsa baliga Dan neman Duniya, ko Kuma ka iske dan uwa na jini matashi yayi Zina da ya'yarsa ko kanwarsa ta jini ko kuma yayi Mata fyde don neman Duniya, ko Kuma ka samu mace Budurwa baliga ko Kuma Matar aure tana lalata da karamin yaro ko Dan uwanta na jini matashi saboda Bokaye da Malaman Tsubbu sun gwada musu cewar ta Haka za,a samu nasarar Tara dukiya ba tareda ansha wahala ba ko Kuma anyi wani aiki Mai wahala ba a tunanin su. Wannan al,ada ce ta dabbobi mutane marasa Imani suka Dauka suka yafa kansu dan Canza tsarin auren da kafa gidan iyali da Kuma lalata Tarbiyyar yara maza da Mata Cikin wannan nahiya tamu.
Ba iya wannan abun ya tsaya ba Yan Mata baligai ana Kama su da karfi da tsiya ayi Musu fyde ba tareda yardan su ko amincewarsu ba sai dai ta Hanyar nuna karfi yayin da wasu Kuma ke amfani da hodar iblis Dan gigitar da mata daga Hankalin su kafin aikata musu irin wannan mummunar aiki.
A Daya bangaren Kuma irin shigar da Yan Mata ke yi na nuna tsaraicin su ga Duniya Yana taka muhimmiyar rawa wajen yi musu fyde zaka iske mace Budurwa ta fito kamar yankar rake ko Ina a jikinta ana Gani Babu wani rufi ko lullubi tana tafiyar hawainiya Cikin maza ko Kuma inda tasan maza Matasa suna taruwa Wanda hakan Yana jawo yawaitar fyde daga Mazajen da keda karfin Sha,awa Wanda basu zuwa wajen Bokaye da Malaman Tsubbu Dan Haka ya Zama wajibi ga iyaye maza da Mata su Lura da irin shigar da ya'yan su Mata ke yi kafin fita daga gida da Wanda suka balaga dama kananan yara Dole a Lura da Sanya musu suturu na mutunci da kamala, ya kamata iyaye su kiyaye Ina yaran su kanana ke zuwa yin wasa a cikin unguwannin da Kuma makwafta a Lura sossai da irin mutanen da ke yawo ko gilmawa a Unguwa idan yara sun fita wasa ba kowa ne ake yarda dashi ba a halin yau.
Bisa ga Al,ada da Kuma tsarin halittar Dan Adam ba zai yiwu mutum Namiji yayi Sha,awar mahaifiyarsa ko yarinyarsa ta cikinsa ko Kuma kanwarsa ta jini ko Kuma yara kanana Wanda basu Kai minzalin balaga ba sai dai idan Shedan da wakilansa Malaman Tsubbu da Bokaye sun kadawa mutum kararrawa Allah ka kiyashe mu.
Kira ga iyaye
Da zarar yarinya ta balaga ta Kai minzalin aure Kuma ta samu manemi ayi kokari a aurar da ita Dan kaucewa zubar Mata da kima da mutuncinta na ya mace, bincike Mai zurfi ya nuna ana yiwa Yan Mata da yawa fyde Amma ba kowa bace ta iya fitowa ta bayyanawa Duniya halin da take ciki ba Kuma akasarin hakan Yana faruwa ne daga manyan mutane Wanda ko anyi karar su ba Lallai bane ayi nasara a wajen Shari,ar dan sun riqe da madafun iko iyaye a kula Sossai Tarbiyyar yara da Allah ya bamu Amana ce a wajen mu Kuma Allah zai tambaye mu ranar Qiyama, a karshe Ina yi Mana Addu,a Allah ya tsare Mana mutuncin mu da Zuriyar mu ya Hana mu bin son Zuciya da rudin shedan.
Wassalamu Alaikum Warahmatullah.
Dan uwanku a musulunci Dalib Umar Muhammad Jassawa
Comments