{MATSALAR TSARO MIYE HAQIQANIN GASKIYAR,} WAZIRI SIDIQIN SHEIKH YUSUF SAMBO RIGACHIKUM HAFIZAHULLAH.





Assalamu Alaikum warahamatullahi wa barakatuhu.

 sako daga bakin mataimakin shugaban majalisan mallamai na kasa

Ashe sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum
Wazeeri siddiqeen, Allah yakara ma Mallam kariya, Imani, tausayi,hakuri, juriya istiqamah, da hangen nesa. Ameen ya Rahaman.

Mallam yace :-

Tabbas muna cikin Damuwa Dangane da zubar da jini da kashe kashe da ke faruwa a Arewacin kasar nan Duk da kuwa mafi rinjayen masu mukami  a harkar tsaron kasa duka yan Arewa ne.

Tun daga kan Shugaban sojojin kasa Burutai dana sama Sadiq Abubakar da shugaban yan sanda na kasa IG P da shugaban Custom na kasa Hamid Ali Da Immigration  Baban Dede Minister Tsaro magashi Da NS A mai baiwa shugaban kasa shawara a harkar tsaro da civil Difance da minister Sharaa da CJN shugaban masu sharaa na kasa da minister sharia.

 Shugaban kasa Dan Arewa Shugaban majalisar Dattijai Sanate President dan Arewa Deputy Speaker  na kasa Dan Arewa Sakataren Gomnatin na kasa Boss mustafa Dan Arewa.

 Amma da haka a kasa shawo kan wannan kashe kashe da akeyi Yan Boko Haram, su kashe  kidnappers,  su kashe yan fashi,  su kashe yan kungiyoyin Asiri, su kashe A can kudancin kasa,

 A koro mutanenmu duk da cewa kananan sanaoi sukeyi a can kudun abinda bai wuci shu shainaba ko dillancin sayarda Dabbobi ko dako,

 Amma su kuma a nan Arewa sunyi Dominant namu a dukkan harkokin kasuwanci da mallakar gurare da gina guraren ibadarsu a yalwace,

 mu kuwa a can kudu bamuma isa a bamu guraren gina wajan ibadarmuba sai dai Tamfurare na ginin kwano ko bachar,  Ku dubi yanda aka kama Dan Arewa aka tafi dashi kotun kudancin kasa aka yi mishi hukuncin daurin shekaru ashirin da biyar 25year dan kadai kurum ya musuluntar da matar da sukayi aure, kuma ita ba yarinya bace Tama haura shekaru sha takwas, wanda tsarin mulkin Dokar kasa ya bata ikon canja addini ko zabin yin abinda takeso,  To amma kuma a daidai lokacin ga kuma wasu an kamasu suna tare yara kanana almajirai da basu wuce shekaru bakwai ko gomaba suna kamesu su tafi dasu kudancin kasa su canza musu suna kuma su canza musu addini, Ga yakar makarantun allo da aka fito dashi maimakon a duba ina kura kuran da ke ciki a gyara .

San nan ga rikicin kabilanci da aka jefa a tsakaninmu dana Rikicin addini .

Ga tsari da aka shigo dashi na raba fulani da akayi da dabbobinsu ga watsi da akayi dasu ba karantarwa ba ilimin Boko Ba na Arabiya.

 Ga rashin girmama juna tsakanin Malamai da al, majrai ko takanin shugabanni da mabiya.

 Ga rashin hadin kai tsakaninmu haka tsakanin masu mulkin da suka gabata da masu yi yanzu

Ga rashin girmama raayin juna.

Ga Rashin fahintar addini na wasu shugabanninmu

Ga son Duniya na wasu daga cikinmu mu malaman addini ga kin karbar shawarar juna akan gaskiya.

 To idan kuma kayi rashin sa'a ya zama shugaban Jamaa a kasa ko a jiha ko a karamar hukuma ko a bangaren masarauta Rainon Yahudu ne da nasara ga kuruciya ga mulki ga kudi ga rashin fahimtar addini ga son zuciya gashi an fito daga karamin gida Tofa sai abinda Allah yayi,   Dan haka dai mu koma ga Allah kuma malamai kuji tsoron Allah ku fito kuyi magana kan halin da ake ciki kamar yanda kukaita magana akan kura kuran da aka tabka a gomnatin baya.

Duk da na zanta da wani gingimemen malami akan haka Wai sai yace mini ai Baayima shugaba Nasiha a bayyane.

To sai nace mishi ai kuwa anyi nasihar a bayyane a gomnatin da ta gabata anyi kuka anyi sinuwa anyi laanta anyi alqunuti an zaburar ko a lokacin baaga Nassin bane?

To da zarar malami ya karkata zuwaga masu mulki dan suna yi mishi abinda ya keso aka bar addinin Allah yana wulanka aka rikabi masallatai tareda malamai ana umurnin a rufe msallatai a bar Sallah Malamai suka koma yan amshin shatar masu mulki Aka koma malamai suna ganar gine gine masu tsada da gasar hawa manyan motoci Son Duniya da tsoron mutuwa ya shiga zukatan musulmi musamman malamai To shikenan kuma sai istirja'i, To Allah ka bamu mafine. Ameen ya Rabbi

Allah yasaka da Alkhairi baban mu,

Comments

Popular posts from this blog

MALAMAN TSUBBU DA BOKAYE SU SUKE INGIZA MASU YIN FYADE

Do you want to know about (COVID19 VIRUS) read this you will be shock

(AREWA LIVES MATTER 13-06-2020)