NASIHA MAI RATSA JIKI TARE DA TAUHIDI DAGA FADILATU SHEIKH MUHAMMAD THANI YAHYA JINGIR
Rahoto daga Mal.Hamza Muhammad Sani
Alhamdulillahi yau juma’a 20/10/1441h-12/
06/2020.
Gamu a gaban shugaban majalisar malamai ta kasa Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir tare da Hafiz Abdurrahman Ahmad suna karantar damu addini.
Cikin karantarwar Malam akwai tauhidi da kuma mu’amalat ta zaman takewar rayuwar al’umma musamman abinda ya shafi rayuwa ta duniya da lahira.
Malam yayi godiya ga Allah(S.W.T)
Kuma ya tabo halin da muke ciki da kuma inda muka sami kammu a yau musamman akan godiya ga Allah akan yadda muka sami kammu a yau na murna ta barka barka,musamman mu anan jihar plateau yadda Gwamnan jihar Barr.Simon Lalong da ya cire mana dokar kulle wanda mu dama namu akwai sauki da fata Allah ya saka masa da alkhairi.
Malam yayi addua ga kasa da al’ummar kasa da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakansa na gaskiya,da gwamnoni da mataimakansu na gaskiya.
Comments